Home Labaru Magudin JAMB: ICPC Ta Fara Gudanar Da Bincike Kan Jarabawar 2019

Magudin JAMB: ICPC Ta Fara Gudanar Da Bincike Kan Jarabawar 2019

323
0

Hukumar yaki da rashawa da sauran ayyuka makamantan su ICPC ta fara gudanar da bincike a kan magudin jarabawar da aka samu a yayin rubuta jarabawar shiga jami’o’i ta kasa JAMB da ta gabata.

Daya daga cikin jami’ar hukumar Mrs Olubukola Balogun ta sanar da hakan ga manema labarai a Abuja, inda ta kara da cewa, hukamar ICPC na kan binciken magudin jarabawar, wanda akwai sa hannun iyayen yara da kuma kungiyar wasu kwararrun masu rubuta jarabawa.

Balogun ta ce, hukumar su na iya bakin kokarin ta domin gano hakikanin gaskiyar lamarin, sannan duk wanda aka samu da laifi za a gurfanar da su a gaban kotu.

Idan dai ba a manata ba, kamfanin dillacin labaran Nijeriya NAN ya ruwaito cewa, shugaban hukumar JAMB Farfesa Ishaq Oloyede ya ce wasu iyayen na biyawa mutane 10 su rubutawa yaron su jarabawa.

Leave a Reply