Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta kama wani mutum mai suna Murtala Muhammad dauke da buhunan kudi hudu da kimanin naira miliyan sittin a jihar Zamfara.
EFCC ta samu nasarar kama mutumin ne bayan ta samu bayanan sirri game da zargin sa da ake yi da safarar makudan kudade.
Jami’an hukumar EFCC sun samu wannan nasara ce a ranar Talatar da ta gabata, a yayin da suka kai samame wani gida da Murtala ya ke zama mai lamba 145 a rukunin gidajen Igala, a Gusau.
Daga cikin abubuwan da jami’am EFCC suka kama akwai wata motar Toyota Land Cruiser Prado, a cikin ta akwai Ghana Must Go guda hudu dauke kudade, wanda adadin kudaden suka tasamma naira miliyan 60.
Haka kuma jami’an hukumar sun gano bindiga guda makare da alburusai da karamar bindiga kiran gida, da kuma wasu alburusai guda 37. A karshe hukumar EFCC ta ce zata gurfanar da murtala Muhammad a gaban kotu da zarar ta kammala gudanar da bincike a kan sa.
You must log in to post a comment.