Home Labaru Bamanga Tukur Ya Ce Shugaba Buhari Shi Kadai Ba Zai Iya Magani...

Bamanga Tukur Ya Ce Shugaba Buhari Shi Kadai Ba Zai Iya Magani Ba

28
0

Tsohon shugaban babbar jam’iyyar adawa a Najeriya PDP, Alhaji Bamanga Tukur ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai iya shawo kan matsalolin Najeriya shi kadai ba.

A cewar Bamanga Tukur, dole ne sai kowa ya sa hannu a al’amuran gyara kasa kafin a iya magance kalubalen Najeriya.

Ya ce mutum daya kadai ba zai iya ba domin ba Buhari bane zai nemi gona ya noma, bas hi ba ne zai je kasuwa ya sayar ya kaya cikin rahusa, dan haka dole kowa ya zamana yana ciki matukar ana son a samu gyara.

Dangane da batun masu kiraye-kirayen a raba Najeriya kuwa, tsohon shugaban jam’iyyar ta PDP ya ce raba Najeriya ba shi ne mafita ba kowa kawai ya gyara halin sa