Home Labaru Korafin Zabe: PDP Ta Taya Gwamna Wike Murnar Samun Nasara A Kotun...

Korafin Zabe: PDP Ta Taya Gwamna Wike Murnar Samun Nasara A Kotun Koli

451
0
Nyesom Wike, Gwamnan Jihar Rivers

Kotun koli ta tabbatar da nasarar Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers, inda ta yi watsi da korafin Awara Festus da jam’iyyar AAC.

Kwamitin alkalai bakwai ne su ka yanke hukuncin, inda su ka tabbatar da abin da kotun sauraren kararrakin zabe ta yanke.

Tun a kotun zaben, alkali ya yi watsi da korafin Festus da jam’iyyarsa AAC, amma hakan bai sa dan takarar ya hakura ba, inda ya zarce zuwa kotun koli domin daukaka kara.

A karshe Kotun kolin ta raba gardama tsakanin Wike na jam’iyyar PDP da Festus na jam’iyyar AAC, inda ta tabbatar da nasarar Wike ta hanyar yin watsi da korafin Festus baki dayansa.

Mai magana da yawun jam’iyyar PDP Kola Ologbondiyan, ya jinjina wa Kotun koli bisa wannan hukunci, ya na mai cewa yanzu ne ‘yan Nijeriya za su kara sanin mahimmancin kotun, kasancewar an kwatanta adalci yayin zartar da hukuncin, kuma ya taya Gwamna Wike murnar wannan babbar nasara da ya samu.

Leave a Reply