Home Labaru Magance Matsalolin Tsaro: Gwamnonin Kudu Maso Yamma Za Su Yi Aiki Tare

Magance Matsalolin Tsaro: Gwamnonin Kudu Maso Yamma Za Su Yi Aiki Tare

330
0

Shugaban gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya ce gwamnonin yankin kudu maso yammacin Najeriya za su yi aiki tare dan magance matsalar tsaro dake addabar Najeriya.

Fayemi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan kammala Lakcar da sashen koyar da aikin jarida na jami’ar na Legas ya shiraya.

Gwamnan ya ce jami’an tsaro da sauran hukumomin da abin ya shafa na yin iya bakin kokarinsu wajen samar da tsaro, amma akwai bukatar kara zage damtse.

Ya ce babban burin gwamnatoci shine su magance wannan matsaloli tare da samar da ayyukan yi da kuma samar da yanayi mai kyau musamman ga masu zuba jari da ‘yan kasuwa.