A ranar Talata mai zuwa ake sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari, zai bude taron ranar ‘yan cin dan Adam da yaki da cin hanci da rashawa, kamar yadda mai rikon mukamin jami’in yada labarai na hukumar EFCC Tony Orilade ya bayyana.
Baya ga shugaba Muhammadu Buhari, Orilade ya ce akwai shugabannin kasashen Rwanda da na Ghana da Liberia da na kasar Senegal da za su halarci taron.
Ya ce a wajen taron, shugaba Kagame zai yi jawabi a kan illar cin hanci da rashawa a lokacin zabubbuka da sayen kuri’u da sauran su.
Daga cikin masu jawabi a wajen taron, akwai tsohon shugaban hukumar zabe zabe ta kasa Farfesa Attahiru Jega, wanda zai yi magana a kan katsalandan da ‘yan siyasa ke yi wa masu kada kuri’a a lokacin zabe.