Home Labaru Sulhu: Gwamna Ganduje Da Sarki Sanusi Sun Fahimci Juna

Sulhu: Gwamna Ganduje Da Sarki Sanusi Sun Fahimci Juna

685
0

Akwai alamu masu karfi da ke nuna cewa rikici tsakanin gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ya zo karshe bayan wata matsaya da aka cimma a birnin Abuja.
A ranar Juma’a ne rahotamnni suka ce shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya shiga lamarin, bayan kiran da ya samu daga dattawan arewa yayinda rikici tsakanin gwamnan da sarkin ke kara daga hakali a jihar.
Sanya bakin Shugaban kasa a lamarin na zuwa ne kwana guda kafin wa’adin da gwamnatin jihar ta ba sarkin ya yi bayani game da zargin da ake wa masarautar ya cika.
A taron sulhun da aka gudanar gwamnan da sarkin sun amince su mai da wukar don rage fargaba domin guje wa karya doka da oda.

Leave a Reply