Ministan yada labarai da al’adu Lai Mohammed, ya roki ‘yan Nijeriya su yafe wa shugaba Muhammadu Buhari a kan batar da takardun makarantar sa na sakandare da ya yi.

Lai Mohammed ya bada hakurin ne a cikin wani bidiyo, yayin da ya yi wata hira da gidan talabijin na Channels Tv.
Karanta Wannan: Takaddama: An Bayyana Wa Kotun Zabe Cewa Shugaba Buhari Ya Yi Jarrabawar Waec
Ministan dai ya bada hakurin ne, bayan an yi masa tambaya game da takardun makarantar shugaba Buhari, inda ya ce Shugaba Buhari ya cancanci a yafe masa, saboda yanzu shekaru 53 kenan da ya kammala makarantar sakandare, kuma bai ma san inda ya ajiye takardun na shi ba.
Wannan dai ya biyo bayan ka-ce-na-cen da ake yi cewa shugaba Buhari bai kammala karatun sa na sakandare ba.
You must log in to post a comment.