Home Labaru Sukar Buhari: Abin Da Ya Sa Ba Mu Daukar Mataki A Kai...

Sukar Buhari: Abin Da Ya Sa Ba Mu Daukar Mataki A Kai – Adesina

358
0
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Mai taimaka wa shugaban kasa ta fuskar yada labarai Femi Adesina, ya ce shugaba Muhammadu Buhari da gwamnatin sa ba su son cin mutuncin da ake yi masa a shafukan sada zumunta, tare da fadin dalilin da ya sa shugaba Buhari bai dauki mataki a kai ba har yanzu.

Femi Adesina
Femi Adesina

Adesina ya bayyana haka ne, yayin wata hira da ya yi da jaridar TheCable, inda ya ce, yayin da wasu ke ganin cewa shugaba Buhari bai damu da masu zagin shi ba, wasu kuma na ganin cewa lokaci ya yi da shugaba Buhari zai dawo Buharin da aka sani a shekara ta 1984.

Kranta Wannan: Gwamnatin Buhari Ba Za Ta Yanke Huldar Jakadanci Da Afirka Ta Kudu Ba – Geoffrey

Adesina ya cigaba cewa, duk masu magana a kafar sadarwa bata lokacin su kawai su ke yi, ya na mai bada misali da cewa, a zaben da ya gabata, duk mai bin kafar sadarwa zai dauka cewa jam’iyyra APC ta fadi.

Ya ce sun riga sun san cewa surutu ne kawai ake yi, don haka idan aka ji irin wadannan surutan a kafar sadarwa a sani cewa wasu ‘yan tsiraru ne kawai.