Home Labaru Zamba A Yanar Gizo: Hukumar EFCC Na Ci-Gaba Da Kame A Nijeriya

Zamba A Yanar Gizo: Hukumar EFCC Na Ci-Gaba Da Kame A Nijeriya

755
0
Zamba A Yanar Gizo: Hukumar EFCC Na Ci-Gaba Da Kame A Nijeriya
Zamba A Yanar Gizo: Hukumar EFCC Na Ci-Gaba Da Kame A Nijeriya

Yayin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta kara zage damtse wajen kamen ‘yan damfara da zamba ta yanar gizo a Nijeriya, lamarin na kara daukar hankali musamman saboda cikin wadanda aka kama har da wasu da hukumar FBI ta kasar Amurka ke nema.

Karanta Wannan: Damfara: EFCC Ta Kama Oyediran Da Kasar Amurka Ke Nema Ruwa A Jallo

Munin lamarin da ya zama ruwan dare gama duniya dai babbar barazana ce ga mutuncin Nijeriya a idon duniya.

Ya zuwa yanzu dai, hukumar EFCC ta yi kame a garuruwan Ilori da Legas da Enugu da wasu manyan biranen Nijeriya.