Home Labaru Dakatar Da Ganduje: APC A Kano Ta Kori Shugabannin Jam’Iyyar A Matakin...

Dakatar Da Ganduje: APC A Kano Ta Kori Shugabannin Jam’Iyyar A Matakin Unguwa

95
0
Ganduje (2)
Ganduje (2)

Kwamitin ayyuka na jam’iyyar APC reshen jihar Kano ya sanar da dakatar da wasu jiga-jigan jam’iyyar a unguwar Ganduje da ke karamar hukumar Dawakin Tofa ta jihar Kanon, wadanda a baya suka sanar da dakatar da shugaban jam’iyyar na kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje, daga jam’iyyar.

Rahoton na cewa, jam’iyyar APC a unguwar Ganduje karamar hukumar Dawakin Tofa ta jihar Kano ta dakatar da shugaban jam’iyyar na kasa  ne bisa zargin da gwamnatin jihar ke yi masa na karbar cin hanci da rashawa.

Sai dai a wani martani da shugabannin jam’iyyar na karamar hukumar suka yi cikin gaggawa, sun yi watsi da dakatarwar tare da korar wadanda ke da hannu wajen dakatar da shugaban jam’iyyar na kasa..

Shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Dawakin Tofa, Inusa Suleiman Dawanau, ya shaida wa manema labarai a Kano a ranar Litinin cewa, wadanda ke da hannu a dakatar da shugaban jam’iyyar APC na kasa, sun shiga cikin bata-gari ne ta hanyar yin zagon kasa ga jam’iyyar APC tare da hadin kai ga jam’iyya mai mulki a jihar.

Baya ga dakatarwar, kwamitin ayyuka na jam’iyyar a matakin jiha, ya kuma sanya wa shugabannin jam’iyyar a unguwar Ganduje takunkumi na tsawon wata shida tare da kafa kwamitin bincike na musamman domin tabbatar da wasu zarge-zarge da ake yi musu.

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, ya ce, sun amince da matakin da shugabannin jam’iyyar a matakin karamar hukumar suka dauka.

Leave a Reply