Home Labaru Mafi Karancin Albashi: Gwamnatin Tarayya Za Ta Gana Da Kungiyar ‘Yan Kwadago

Mafi Karancin Albashi: Gwamnatin Tarayya Za Ta Gana Da Kungiyar ‘Yan Kwadago

615
0

Gwamnatin tarayya da gamayyar kungiyar kwadago za su zauna domin kawo karshe akan maganar mafi karancin albashin ma’aikata.

Ana sa ran za a cimma matsaya guda wadda kuma za ta kasance ta karshe bayan wannan ganawar.

Ministan kwadago Chris Ngige

Ministan kwadago Chris Ngige, ya shaidawa manema labarai  cewa maganar mafi karancin albashi ita ce kan gaba a cikin ayyukan da zai fara yi, da zarar ya shiga ofishi.

A yayinda ma’aikata da ke a matakin na 7 zuwa 14 ke neman karin kashi 30 da kuma wadanda ke mataki na 15 zuwa 17 suna neman karin 25 gwamnati na yi masu ta yin karin kashi 9 ne da kuma 5.

Har yanzu dai an kasa cimma matsaya guda wadda za ta bada damar fara biyan sabon mafi karancin albashi da shugaban kasa ya rattabawa hannu ranar 18 ga watan Afrilu.