Home Labaru Yaki Da Ta’addanci: Wasu Jami’an Tsaro Na Kawo Cikas- Badmus

Yaki Da Ta’addanci: Wasu Jami’an Tsaro Na Kawo Cikas- Badmus

228
0

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yi ikirarin cewa wasu masu neman kawo cikas ga yaki da ta’addanci a hukumomin tsaron Najeriya na aiki domin ganin ba a kawo karshe kallubalen tsaro ba.

Kakakin Rundunar ‘yan sanda mai kula da shiyya ta 2 Dolapo Badmus

Kakakin Rundunar ‘yan sanda mai kula da shiyya ta 2 Dolapo Badmus, ta yi ikirarin cewa wadanda ke kawo cikas ga yaki da ta’addanci a Najeriya sun mayar da hankali ne kan tara dukiya.

Badmus, ta ce an gaza cin galaba kan yaki da ta’addanci a Najeriya ne, saboda hukumomin tsaro su na yi wa junan su zagon kasa.

A yayin da ta ke alla-wadai ga wadanda ke kawo cikas ga yaki da ta’addancin, ta ce abin bakin ciki ne yadda wasu suka ba mai laifin da aka kama damar tserewa.

Ta kara da cewa baya ga tserewar mai laifin, an kuma yi asarar rayyuka mutum biyar, 3 ‘yan sanda da mutane biyu masu ba su bayyanai.

Badmus ta ce, yayin da wasu jami’an tsaro ke aiki dare da rana domin kawo karshen garkuwa da mutane, da fashi da makami da kuma ta’addanci, wasu na nan suna yi musu zagon kasa saboda abinda za su samu.

Kakakin Rundunar Dolapo Badmus, ta yabawa rundunar ‘yan sandan da jami’an ta kan binciken da ake gudanarwa bayan kisan ‘yan sanda a Taraba.