Home Labaru Kiwon Lafiya Ma’aikatan Kiwon Lafiya A Jihar Bauchi Za Su Fara Yajin Aiki

Ma’aikatan Kiwon Lafiya A Jihar Bauchi Za Su Fara Yajin Aiki

56
0

Kungiyar ma’aikatan Lafiya a jihar Bauchi, sun fara shirin shiga yajin aikin Sai-Baba-Ta-Gani, inda su ka ba Gwamnatin Jihar wa’adin makonni biyu ta cika alkawarin da ke tsakanin ta da kungiyar.

‘Yan kungiyar sun kara da cewa, idan har ba a cika masu alkwarin ba za su umurci ‘ya’yan kungiyar su fara yajin aiki, su kuma kaurace wa duk wasu asibitocin gwamnati.

A wani taron ‘yan Jarida da su ka gudanar, Shugaban kungiyar Kwamrade Yusuf Aliyu Fada, ya ce dalilin halin kunci da ‘ya’yan kungiyar ke fuskanta, ya sa dole su gabatar da wannan bayanin da kuma neman mahukunta su kale su da idon rahama, domin sun kwashe gomman shekaru su na aiki amma ba a ba su ko da sisin kwabo ba.

Kwamrade Yusuf ya kara da cewa, a duk lokacin da su ka yi alkawari da gwamnati ba a cikawa, don haka su ke bukatar wannan karon ya zama lokacin da za a kyautata rayuwar ma’aikatan lafiya a jihar.

A na shi bangaren,Kwamishinan Lafiya na Jihar Bauchi Dr. Samaila Dahuwa ya ba ‘yan kungiyar hakuri, tare da ba su tabbacin mika koken su zuwa ga Gwamnan Jihar.