Home Labaru Ilimi Gwamnatin Zulum Ta Raba Wa Yaran Makaranta Keken Hawa 6000 A Borno

Gwamnatin Zulum Ta Raba Wa Yaran Makaranta Keken Hawa 6000 A Borno

67
0

A wani yunkuri na hana dalibai zuwa makaranta a makare, gwamnatin jihar Barno ta raba wa daliban da ke zuwa makarantun sakandare na Je-Ka-Ka-Dawo kekunan hawa dubu 6 a wasu kauyukan jihar.

Kwamishinan ilimi na jihar Abba Wakilbe ya sanar da haka, a wajen taron bude makarantar koyar da fasaha da gwamnati ta gina a Wuyo da ke karamar hukumar Bayo.

Wakilbe, ya ce bayan haka, gwamnatin ta kuma samar da kekuna 300 domin raba wa daliban da za su rika zuwa karatu a makarantar, ta kuma bada littatafai dubu 231 domin a raba wa duk makarantun da ke fadin jihar.

Kwamishinan ya cigaba da cewa, a cikin shekara biyu, gwamnatin Zulum ta gina makarantu 21 a jihar, inda a ciki akwai makarantun koyar da fasaha guda hudu.

Ya ce Gwamna Zulum ya bada umurin zuba ingantattun kayan aiki da kwararrun malamai a makarantun, domin sama wa dalibai ilimin Boko ingantacce a ko da yaushe.