Home Labaru Kasuwanci Makomar Kudaden Tallafin Mai Ta Janyo Muhawara Ciki Da Wajen Nijeriya

Makomar Kudaden Tallafin Mai Ta Janyo Muhawara Ciki Da Wajen Nijeriya

87
0

Shirin kawo karshen tallafin man fetur da kuma karkatar da kudaden tallafin domin raba wa marasa karfi na ci-gaba da haifar da muhawara ciki da wajen Nijeriya.

Wata majiya ta ce, Shirin gwamnati na raba wa talakawa tallafin zai rika lakume akalla naira tiriliyan 2 da biliyan 400 a kowace shekara.

Ministar kudi Zainab Ahmed, ta ce gwamnati za ta raba wa mutane akalla miliyan 40 naira dubu biyar-biyar a kowane wata, shirin da zai fara daga watan Yuli na shekara ta 2022, lokacin da tallafin man fetur zai kare.

Da dama dai sun nuna fargaba da cewa, ba lallai ba ne kudaden tallafin su isa ga jama’a, musamman marasa karfin da aka yi nufin saukaka mawa a kan halin da za su shiga.

Sai dai ministar kudi Zainab Ahmed, ta ce gwamnati za ta tabbatar da biyan kudaden ga wadanda su ka cancanta ta hanyar amfani da lambobin tantancewa da katin shaidar zama dan kasa, da kuma lambar asusun banki, kuma za a aiwatar da shirin ne tare da hadin gwiwar Bankin Duniya.