Home Labaru Lula Da Silva: An Sako Tsohon Shugaban Brazil Daga Kurkuku

Lula Da Silva: An Sako Tsohon Shugaban Brazil Daga Kurkuku

183
0

Kotu ta saki tsohon shugaban Brazil Lula Da Silva, bayan ya shafe tsawon shekara daya da rabi a gidan yari.

Dubban magoya baya ne su ka yi ma shi maraba a harabar ofishin ‘yan sanda a birnin Curitiba.

Mista Lula dai ya na kalubalantar hukuncin da aka yanke ma shi na daurin shekaru tara bisa zargin cin hanci.

Sai dai tsohon shugaban kasar ya ce, wani bi-ta-da-kullin siyasa ne da aka bullo da shi domin hana shi takara a zaben da za a yi a shekara mai zuwa.

Kawo yanzu dai shugaba Jair Bolsonaro bai ce komai game da sakin Mista Lula da Silva ba.