Home Labaru Kiwon Lafiya Likitocin Najeriya Mazauna Ƙetare Sun Yi Ƙorafi Kan Dokar Hana Likitoci Fita...

Likitocin Najeriya Mazauna Ƙetare Sun Yi Ƙorafi Kan Dokar Hana Likitoci Fita Waje

1
0

Ƙungiyar kwararrun likitoci da likitocin haƙora da ke aiki a
ƙasashen waje, ta shigar da ƙorafi ga Majalisar Dokoki ta
tarayya, a kan ƙudurin da ke neman hana likitocin neman aiki
a ƙasashen ƙetare har sai sun yi wa Nijeriya hidima ta tsawon
shekaru biyar.

Rahotanni sun ce kungiyar ta aika wa kakakin Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila wasiƙar, sannan ta aike wa shugaban Majalisar Dattawa da shugaban kwamitin lafiya na Majalisar Dakta Ibrahim Oloriegbe da kDakta Tanko Sununu kwafin wasikar.

Kungiyar, ta ce ƙudurin da Ganiyi Johson ya bijiro da shi, babu abin da zai janyo sai ci baya, kuma ba zai hana kwararrun likitocin ficewa daga Nijeriya ba.

Ta ce babban abin da ke janyo matsalar shi ne rashin kyakkyawan tsari ga ɓangaren lafiya da kuma ƙin zuba kuɗaɗe a ɓangaren lafiya, ta na mai cewa tsarin Nijeriya ba ya taimaka wa kwararru ko haɓɓaka kwarewar su.