Home Labaru Tinubu Da Uwargidan Sa Sun Raba Wa Talakawan Abuja Musulmai Da Kiristoci...

Tinubu Da Uwargidan Sa Sun Raba Wa Talakawan Abuja Musulmai Da Kiristoci Abinci

72
0

Zababben Shugaban kasa Bola Tinubu da uwargidan sa
Oluremi, sun raba wa Musulmai da Kiristoci dubu 100 kayan
abinci a Abuja.

Shugabar mata ta jami’iyyar APC Betta Edu ce ta raba kayan a madadin Tinubu da uwargidan sa.

Yayin da take rabon kayan abincin a babban masallacin Abuja, Edu ta ce an raba abincin ne domin tallafa wa mutane a Lokacin azumin Ramadan da kuma bikin Easter.

Ta ce raba abincin zai taimaka wajen karkato da hankalin mutane wajen son juna da inganta zaman lafiya tare da yi wa kasar nan addu’o’i musamman a wannan lokaci.

Leave a Reply