Home Labaru Libiya: An Keta Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Kasa Da Sa’a 24

Libiya: An Keta Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Kasa Da Sa’a 24

306
0
Libiya: An Keta Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Kasa Da Sa'a 24
Libiya: An Keta Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Kasa Da Sa'a 24

Bangarorin da ke yakin basasa tsakanin su a Libiya, sun keta yarjejeniyar tsagaita wutar da su ka cimmawa.

Dukka bangarorin biyu dai su na zargin junan su da keta yarjejeniyar sa’o’i kadan bayan ta fara aiki.

Tun da farko dai, bangarorin biyu sun amince da tsagaita wuta sakamakon matsin lambar da su ka samu daga masu goya masu baya wato Turkiyya da Rasha.

Akwai bangaren Janar Khalifa Haftar, wanda ke samun goyon baya daga kasar Rasha, da kuma bangaren gwamnatin Tripoli da Majalisar Dinkin Duniya ke jagoranta.

A baya dai bangaren Janar Haftar sun yi watsi da kiran da aka yi na yin sulhu, yanzu haka kuma sun ce za su tsagaita wuta idan daya bangaren ‘ya bi yarjejeniyar tsagaita wutar yadda ya dace’.

A nata bangaren, gwamnatin Tripoli ta bayyana cewa, za ta tsagaita wuta daga ranar Lahadin nan ne.