Home Labaru Sojan Nijar 89 Ne Su Ka Mutu A Harin Shinagodar

Sojan Nijar 89 Ne Su Ka Mutu A Harin Shinagodar

736
0
Sojan Nijar 89 Ne Su Ka Mutu A Harin Shinagodar
Sojan Nijar 89 Ne Su Ka Mutu A Harin Shinagodar

Kwanaki uku, biyo bayan kazamin harin da yan ta’adda su ka kai barikin sojin Shinagoda daf da kan iyaka da kasar Mali, rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na nuni da cewa gawarwakin sojin kasar 89 ne aka binne a makabarta.

A Ranar Larabar da ta gabata, rundunar Sojin Nijar ta tabbatar da harin garin Shinegoda a kan iyakar kasar da Mali, wanda ya hallaka mata dakaru da dama, duk da dai ta bayyana yadda dakarun ta na sama su ka maida martanin farmakin tare da hallaka ‘yan ta’adda sama da 60.

A ranar Litinin mai zuwa ne, Shugaban kasar Mahamadu Issufu zai halarci taro a garin Pau na kasar Faransa da wasu shugabanin kasashen yankin Sahel, domin tattaunawa da shugaban Faransa Emmanuel macron dangane da makomar dakarun Faransa a yankin Sahel. Al’umomin kasashen yankin Sahel musamman Mali da Nijar, sun bayyana adawar su dangane da kasancewar dakarun Faransa a kasashen su.