Hukumar da ke sa ido kan harkar sadarwa ta Najeriya, NCC ta
tabbatar da rufe layukan masu wayoyin salular da basu haɗa da
lambar shaidar zama ɗanƙasa ba.
A makon da ya wuce ne hukumar ta ba kamfanonin wayoyin salula umarnin rufe layin duk wani wanda bai haɗa layin wayarsa da NIN ba ya zuwa ranar 28 ga watan Fabairun, 2024.
Wasu kafofin yada labarai na ƙasar nan sun ce waɗanda lamarin ya shafa sun kai miliyan 11 da dubu 200. Sai dai wata hira da wani gidan talabijin na cikin ƙasar, kakakin hukumar , Reuben Muoka ya ce zai yi wuya a ce ga yawan layukan da aka rufe, amma NCC za ta yi kididdiga kafin ƙarshen wannan makon, bayan sun samu alƙaluma daga kamfanonin sadarwar.
Ya ca an ɗauka cewa duk wani wanda bai bayar da NIN ɗinsa ba an rufe layinsa ,amma haƙiƙanin gaskiya tun kafin cikar wa’adin wasu kamfanonin sadarwan suka fara rufe layukan mutane