Gwamnatin tarayya ta ce za ta fara raba hatsi a faɗin ƙasar a
wani mataki na rage matsin rayuwa da ƴan Najeriya suke ciki.
Ministan aikin gona Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.
Ministan ya ce ya na ba ƴan Najeriya da suke cikin halin matsin rayuwa haƙuri, ya san halin ƙunci da ake ciki, musamman ganin fasa rumbunan abinci da kuma wawaso da aka yi.
Ya ce yana son ya tabbatarwa ƴan Najeriya cewa gwamnati na ci gaba da ƙoƙari na ganin abubuwa sun kyautata.
Sanata Kyari ya ce shugaban ƙasa ya amince a fara raba hatsi da ya kai tan 42,000 a faɗin jihohi 36 na ƙasar a wannan mako.