Home Labaru Lalata Da Dalibai: Kwalejin Tarayya A Jihar Bauchi Ta Kori Malaman Da...

Lalata Da Dalibai: Kwalejin Tarayya A Jihar Bauchi Ta Kori Malaman Da Aka Zarga

149
0
Hukumar kwalejin gwamnatin tarayya a Jihar Bauchi ta kori malamai biyu sakamakon kama su da laifin cin zarafi ta hanyar lalata da ɗalibai mata.

Hukumar kwalejin gwamnatin tarayya a Jihar Bauchi ta kori malamai biyu sakamakon kama su da laifin cin zarafi ta hanyar lalata da ɗalibai mata.

Shugaban kwalejin, Sanusi Gumau, da ya tabbatar da haka ga manema labarai ya ce an ɗauki matakin ne yayin zaman majalisar zartarwar kwalejin na 98 da suka yi a ranar Asabar.

Sanusi Gumau ya ce bayan samun ƙorafi daga ɗaliban, an kafa kwamatoci da zummar bincikar zarge-zargen waɗanda rahoton su ne ya nuna cewa sun aikata laifin.

Ya ce dokokin kwalejin sun bayyana cewa idan aka samu zargi mai girma irin wannan matakin farko da ake ɗauka shi ne bincike zarar an kama malami da laifi kuma hukuncin sa shi ne kora.

Leave a Reply