Home Labaru Harin Goronyo: Gwamnonin Arewa Sun Bayar Da Gudunmawar Naira Miliyan 20 Ga...

Harin Goronyo: Gwamnonin Arewa Sun Bayar Da Gudunmawar Naira Miliyan 20 Ga Iyalan Wadanda Aka Kashe

5
0
Gwamnonin yankin Arewa maso Gabas a Najeriya sun bayar da gudunmawar Naira miliyan 20, ga iyalan waɗanda ‘yan bindiga su ka kashe a kasuwar Goronyo ta Jihar Sakwkwato.

Gwamnonin yankin Arewa maso Gabas a Najeriya sun bayar da gudunmawar Naira miliyan 20, ga iyalan waɗanda ‘yan bindiga su ka kashe a kasuwar Goronyo ta Jihar Sakwkwato.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga yadda masu garkuwa da mutane su ka kai hari a kasuwar Goronyo, a ranar 17 ga watan Oktoba, su ka kashe mutum 49 tare da jikkata da dama cikin masu cin kasuwa.

Sai dai kuma wani rahoto da jaridar Daily Trust ta buga, bayan kwana biyu da kashe mutanen, ta ruwaito gogarman mai safarar manyan bindigogi Shehu Rakeb ya ce sun kai harin ne a matsayin ramuwar-gayyar kisan Fulani su 22 da aka yi a Unguwar Lalle, a lokacin da su ke Sallah.

Shehu Rakeb ya ce waɗanda ‘yan banga su ka kashe Fulani ne, amma ba ‘yan bindiga ba ne.

Yayin bayar da tallafin kuɗin, Gwamna Babagana Zulum, day a mika kuɗaɗen a madadin sauran gwamnonin yankin Arewa maso Gabas, da takwaran sa Inuwa Yahaya na Jihar Gombe sun mika ta’aziyyar su ga gwamnatin jihar da kuma al’umma baki daya.

A nashi bangaren gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sakwkwato ya nuna godiyar sa matuƙa, Inda ya ce ‘yan bindigar sun yi kaka-gida a Jihar Sokoto bayan sun tsere daga ɓarin wutar da Sojoji ke yi masu ne a Jihar Zamfara.