Home Labaru Ilimi Ciyar Da Dalibai: Gwamnatin Tarayya Ta Raba Kwanoni Da Cokula 1,482 Ga...

Ciyar Da Dalibai: Gwamnatin Tarayya Ta Raba Kwanoni Da Cokula 1,482 Ga ’Yan Firamare A Jigawa

524
0

Gwamnatin tarayya ta samar da kwanonin tasa da cokulan cin abinci ga yara ‘yan firamare dubu 13 da 482 a Jihar Jigawa a Karkashin Shirin Ciyar da Dalibai Abinci.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, jami’in shirin ciyar da dalibai na yankin Shehu Baba ne ya damka kayayyakin ga masu dafa abinci 149 a Karamar Hukumar Birniwa.

Da ya ke jawabi a wajen raba kayayyakin, Baba ya ce za a ajiye kwanonin da cokulan a wajen shugabannin da ke dafa abinci domin a rika amfani da su yadda ya dace.

Shehu Baba ya kara da cewa, an samar da wannan tsari a makarantu 106 na yankin, a wani mataki na tabbatar da dalibai sun a cin abinci a cikin wari mai tsafta.

A karshe ya umarci dukkan shugabannin makarantun su kai masa rahoton duk uwar-tuwon da ta zuba wa yara abinci a cikin kwano maras tsafta.

Shirin ciyar da dalibai dai ya na daya daga cikin tsare-tsaren da gwamnatin tarayya ta fito da shi domin rage wa masu karafin karfi radadin kuncin rayuwa.