Home Labarai Kyautar Motoci Da Buhari Ya Bai Wa Nijar Ta Harzuƙa Wasu ‘Yan Nijeriya

Kyautar Motoci Da Buhari Ya Bai Wa Nijar Ta Harzuƙa Wasu ‘Yan Nijeriya

58
0

Ana ci-gaba da maida zafafan martani, biyo bayan matakin gwamnatin Nijeriya ta dauka na tallafa wa Jamhuriyar Nijar da motocin da su ka kai darajar akalla naira biliyan ɗaya da rabi.

Gwamnatin tarayya dai ta ce ta ba maƙwabciyar ta motocin 10 ne da zummar inganta ayyukan tsaro, a daidai lokacin da Nijeriya ke fuskantar matsalolin tsaro a fadin kasar.

Ministar Kuɗi Zainab Shamsuna Ahmed ta shaida wa manema labarai cewa, an ɗauki matakin ne domin a taimaka wa Nijar ta inganta tsaron iyakar ta da Nijeriya.

Ta ce an ɗauki lokaci Nijeriya ta na tallafa wa makwabtan ta, musamman ma mafiya kusanci da nufin karfafa su domin su kare kasashen su ta bangaren da ka iya shafar Nijeriya, kuma ba
wannan ne karo na farko da ta ta taimaka wa Nijar ko Kamaru ko Chadi ba.