Home Labarai Atiku Ya Sake Bada Tabbacin Bayar Da Kaso 40 Na Mukamai Ga...

Atiku Ya Sake Bada Tabbacin Bayar Da Kaso 40 Na Mukamai Ga Matasa Da Mata

457
0

Dan Takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya ba matasan Nijeriya tabbacin bar masu kyakkyawan tarihi idan aka ba shi damar jagorantar al’amuran Nijeriya.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka ma shi ta fuskar yada labarai Abdulrasheed Shehu ya raba wa manema labarai, Atiku Abubakar ya bada tabbacin ne, yayin da ya karbi bakuncin tawagar shugannin PDP sabon karni a karkashin jagorancin shugaban ta Audu Mahmud a gidan sa da ke Abuja.

Tsohon mataimakin shugaban kasar, ya sake jaddada aniyar sa kamar yadda ta ke kunshe a cikin kundin manufofin sa, na ba matasa dama a gwamnatin sa ta hanyar ware masu kashi 40 cikin 100, ya na mai cewa zai yi sauye-sauyen da su ka dace domin bada dama ga mata da matasa.

Wazirin Adamawa ya kara da cewa, a gwamnatin PDP ne kawai aka aiwatar da tsarin kebe wa mata kaso 35 cikin 100, inda ya ce APC ba ta taba girmama wannan yarjejeniyar ba.

Atiku Abubakar, ya kuma koka game da halin da matasa su ka tsinci kansu, amma ya yi alkawarin daidaita al’amuran, don haka, ya ce ilimi zai zamo babban ginshikin gwamnatin sa domin bunkasa rayuwar matasa tare da habbaka dimukuradiyya.

LEAVE A REPLY