Home Labaru Kyakkyawan Mulki: Matasa Sun Bukaci Buhari Ya Bar Boss Mutapha A Kan...

Kyakkyawan Mulki: Matasa Sun Bukaci Buhari Ya Bar Boss Mutapha A Kan Mukamin Sa

299
0

An bayyana sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha a matsayin kashin bayan gwamnatin shugaba Buhari, musamman duba da kwarewar sa a matsayin lauya kuma masani a fannin harkokin kasuwanci da ilimin gudanar da mulki.

Bayanin hakan, ya na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadakar kungiyar matasan Nijeriya da kungiyoyi masu zaman kan su ta raba wa manema labarai, dauke da sa hannun babban jami’in ta na kasa Kwamred Nuhu Lere, bayan wani taro da su ka gudanar a Kano.

Kungiyoyin dai sun bukaci shugaba Buhari ya cigaba da tafiya tare da Boss Mustapha a matsayin sakataren gwamnatin tarayya, duba da irin gagarumar rawar da ya ke takawa ta fuskar ganin Nijeriya ta cigaba a kowane fanni.

Kwamred Nuhu Lere, ya ce Boss Mustapha ya taka rawar gani, musamman duba da yadda ya tsarkake alakar da ke tsakanin bangaren zartarwa da na shari’a da kuma bangaren majalisun dokoki na tarayya