Gwamnan jihar Zamfara mai barin gado Abdul-Aziz Yari ya amince da hukuncin kotun koli, tare da yi wa wanda zai gaje shi fatan alheri.
Yayin da ya ke jagorantar shan ruwa na karshe tare da kwamishinoni da manyan kushoshin gwamnatin sa a gidan sa da ke Talatar Mafara, Yari ya ce sun aminta, sun kuma yarda da hukuncin Allah.
A ranar juma’ar da ta gabata ne, kotun koli ta yanke hukuncin cewa, jam’iyyar APC ba ta yi sahihin zaben fidda gwani ba, lamarin da ya yi sanadiyyar soke kuri’un da jam’iyyar ta samu a dukkan kujerun da ta lashe a zaben a jihar Zamfara.
Tuni dai Hukumar zabe ta tabbatar da ‘yan takarar jam’iyyar PDP da su ka zo na biyu a matsayin wadanda su ka lashe zaben gwamna da na ‘yan majalisun Tarayya da na jiha.
Gwamna Yari, ya ce yarda zaben da aka yi akwai kura-kurai a ciki, ya na mai cewa sun yarda da hukuncin kotun koli, domin lamari ne da Allah ya riga ya tsara.