Home Labaru Sayen Gidan Sauro: A’isha Buhari Ta Kalubalanci Gwamnatin Tarayya

Sayen Gidan Sauro: A’isha Buhari Ta Kalubalanci Gwamnatin Tarayya

301
0
Aisha Buhari Ta Bada Talafin Kayan Aiki Da Abinci Domin Yaki Da Covid-19 A Jihar Nasarawa
Aisha Buhari Ta Bada Talafin Kayan Aiki Da Abinci Domin Yaki Da Covid-19 A Jihar Nasarawa

Uwargidan shugaban kasa A’isha Buhari, ta yi wa gwamnatin tarayya raddi, dangane da yadda ta batar da kimanin Dala miliyan 16 domin samar da gidajen sauro a fadin Nijeriya.

A’isha Buhari ta yi raddin ne, yayin wani taron kara wa juna sani na Mata da aka gudanar a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Uwr gidan shugaban kasar, ta ce shirye-shiryen bada tallafi da gwamnatin tarayya ta assassa da nufin inganta jin dadin rayuwar al’umma, ba ya da wani tasiri a yankin Arewacin Nijeriya.

Yayin da ta ke tabbatar da yadda gwamnatin tarayya ta batar da dalar miliyan 16 wajen sayen gidajen sauro, A’isha Buhari ta ce har yanzu babu wanda ya amfana da gidajen sauron, musamman a mahaifar ta jihar Adamawa.

Duk da mika kokon barar ta da kuma shigar da bukatar neman kason ta na gidajen sauron domin al’ummar mahaifar ta, A’isha Buhari ta ce har yau lamarin ya zama tamkar an aiki Bawa garin su.