Home Labaru Kwazo: Matashi Ɗan Arewacin Najeriya Ya Samu Matsayi A Tarayyar Turai

Kwazo: Matashi Ɗan Arewacin Najeriya Ya Samu Matsayi A Tarayyar Turai

11
0
European-Union

Wani ɗan Najeriya ya shiga jerin wasu matasa 25 da kungiyar Tarayyar Turai EU ta zaɓa a sassa daban-daban na duniya don su riƙa ba ta shawarwari kan harkokin ƙawancen ta da ƙasashen duniya.

Matasahin da ya fito daga jihar Yobe a Arewa maso gabashin Najeriya an zaɓo shi ne da nufin sake ba wa matasa dama a harkokin diflomasiyar duniya.

An zaɓi Imrana Alhaji Buba na ƙungiyar Matasa masu yaƙi da ta’addanci wato Youths Initiative against Terrorism a ƙarƙashin wani shirin Tarayyar Turai na ƙarfafa gwiwar matasa ne.

Tarayyar Turai ta ce shirin mai suna Youth Sounding Board na da nufin ƙirƙirar wani sahihi kuma dawwamammen sauyi kan yadda ƙungiyar EU ke tuntuɓar matasa a cikin ayyukanta na haɗin gwiwa don raya ƙasashe.

Matashin ya shaida cewa wannan dama ce a gareshi wajen isar da sakon matasa kai-tsaye da cimma duk wani bukatu na ci gaban matasa da koken su.