Home Labaru Zarafin Budurwa: Boateng Zai Biya Tarar Euro Miliyan 1.8

Zarafin Budurwa: Boateng Zai Biya Tarar Euro Miliyan 1.8

11
0
Boateng

Wata kotun Jamus da ke birnin Munich ta ci tarar dan wasan Jamus Jerome Boateng euro miliyan 1 da dubu 800, kwatankwacin dala miliyan 2, bayan da ta same shi da laifin cin zarafin tsohuwar budurwar sa.

Dan wasan mai shekaru 33, wanda ya kulla yarjejeniya da kungiyar Lyon ta Faransa a makon da ya gabata bayan ya shafe shekaru 10 a Bayern Munich, an same shi da laifin cin zarafin mahaifiyar ‘yan tagwayen sa mai suna Sherin Senler ne, a yayin hutun da suka yi a yankin Caribbean shekaru 3 da suka gabata. 

Kafin zartas da hukuncin Mai gabatar da kara Stefanie Eckert ta nemi yiwa dan wasan na Jamus daurin talala ne na tsawon 18, kuma ya biya tarar euro miliyan daya da rabi kan cutar da abokiyar zamansa da yayi, zargin da Boeteng ya musanta a baya.

Tsohuwar budurwar fitaccen dan kwallon ta fadawa kotu cewar karfin naushin da tsohon sahibin nata ya dirka mata sai da ya janyo rasa numfashin ta na dan lokaci, bayan da cacar baka ta yi zafi tsakanin su.

Lamarin ya faru ne makwanni bayan gasar cin kofin duniya a Rasha, lokacin da aka fitar da tawagar Jamus a matakin rukuni.