Home Labaru Kwarewar Aiki: ‘Yan Sanda Sun Cire Bama-Bamai Da Aka Dasa Tun Lokacin...

Kwarewar Aiki: ‘Yan Sanda Sun Cire Bama-Bamai Da Aka Dasa Tun Lokacin Yakin Basasa

473
0

Kwararrun ‘yan sanda wajen cire bama-bamai sun ce sun cire wasu bama-bamai a wurare 10 mabambanta da aka dasa tun a lokacin yakin basasa.

Kwamishinan ‘yan sandan, Maikudi Shehu, wanda ya jagoranci  cire bama-baman cikin tsawon watanni biyar, ya tabbatad da haka a yayin wani taro da hukumar tayi a Ikeja.

Maikudi Shehu, ya ce mafi yawan bama-baman an same su ne a wuraren da ake gine-gine, bayan maginan sun sanar da ‘yan sanda, kuma suka tabbatar da an cire su ba tare da sun illata kowa ba.

Kwamishinan ‘yan sandan ya hori mutane su rika hanzarta sanar da hukuma mafi kusa duk wani abun da basu gane masa ba, sai ya tabbatar da cewa ma’aikatan sa baza suyi kasa a guiwa ba wajen daukar matakin da ya dace.

Ya ce bama-baman da aka ciren an dasa su ne tun a lokacin yakin basasan Najeriya a jihohin Imo, da Anambra da kuma Delta.