Home Labaru Karin Albashi : Har Yanzun ‘Yan Sanda Sun Ji Shiru Bayan Watanni...

Karin Albashi : Har Yanzun ‘Yan Sanda Sun Ji Shiru Bayan Watanni 10

1359
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan karin albashi jami’an ‘yan sandan Najeriya, amma har yanzu ‘yan sandan sun ce ba su fara amfana da sabon albashin ba, bayan watanni goma kenan.

A wani binciken da aka gudanar ya ce  jami’an ‘yan sandan har yanzu dai ana biyan su ne da tsohon albashi, bayan shugaban kasa ya rattaba hannun akai.

Rattaba hannu da shugaban kasa ya yi na nufin cewa albashin jami’an ‘yan sanda zai karu a kowane mataki wanda ya hada da alawus da kuma fansho.

Sai dai wasu kanana da kuma manyan jami’an ‘yan sandan da suka zanta da manema labarai a Abuja, sun ce maganar karin albashin ba komai ba ce illa labarin kanzon kurege.

Da yake magana da ‘yan jarida akan wannan al’amari wani jami’in ‘yan sanda mai mukamin ASP wanda ke aiki a Abuja, ya ce, rashin fara biyan su, sabon albashin ya tabbatar da cewa gwamnati ba ta damu da jin dadi da walwalar ‘yan sanda ba.