Home Labaru Kwankwanso Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ba Za A Ba ‘Yan...

Kwankwanso Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ba Za A Ba ‘Yan Kudu Dama Ba

35
0

Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce ba ya son a kai tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a shekara ta 2023 zuwa Kudancin Nijeriya.

Kwankwaso ya bayyana haka ne, a wata hira da ya yi da gidan Talabijin na Channels, inda ya yi magana a kan matsalolin siyasa da dama gabanin zaben shekara ta 2023.

Sanatan, ya yi Allah-Wadai da dagewar da kungiyar gwamnonin kudancin Nijeriya ta yi cewa dole shugaban kasa na gaba ya fito daga yankin su ta kowace hanya.

Kwankwaso, ya kuma dauki kiran da gwamnonin da sauran shugabanin su ka yi a matsayin wani yunkuri na tsorata yankin Arewa domin ya sauke kudurin tsayawa takara.

A karshe Sanatan ya ce, kamata ya yi a yanke shawarar tsayawa takara bisa dabaru ba wai ta hauragiya ko son zuciya ba.