Home Labaru Ilimi Kwalejin Fasaha Ta Kone Wayoyin Dalibai Sama Da 1, 000

Kwalejin Fasaha Ta Kone Wayoyin Dalibai Sama Da 1, 000

688
0

Kwalejin kimiyya da fasaha ta Badun, wato Ibadan Polytechnic, ta kone wayoyin dalibai sama da guda 1,000, wadanda ta kwace a lokacin da dalibai ke rubuta jarabawa a kwalejin a lokuta da dama.

Rahotanni sun ce an kwace wayoyin ne daga hannun dalibai daban-daban a lokutan da ake gudanar da jarabawa a makarantar cikin shekarar da ta gabata domin a rage matsalar satar jarabawa ta hanyar kafofin sadarwa na zamani a kwalejin.

Karanta Labaru Masu Alaka: Gwamnatin Tarayya Ta Ware Biliyan 208 Don Bunkasa Makarantu – Bogoro

Tsohon Mataimakin Shugaban Kwalejin, Bayo Oyeleke, da wani babban malamin makarantar suka bayyana ha a lokacin da suka wakilci makarantar domin sa ido wurin tabbatar da ganin an kone wayoyin.

Bayo Oyeleke, ya shaida cewa hukumar makaranta ta hana dalibai shiga da wayoyi dakin jarabawa, amma kuma suka yi watsi da dokar, ya ce saboda sun ki bin doka ne humumar makaranta ta yankec shawarar rika kwace wayoyin ta na konewa.Ya kara da cewa a kowane lokaci ana gargadin dalibai kada wanda ya sake shiga dakin rubuta jarabawa da wayar hannu domin duk wanda aka kama za’a kone wayar sa.

Leave a Reply