Home Labaru An Yi Kuka Da Ni A Zamfara – Inji Yariman Bakura

An Yi Kuka Da Ni A Zamfara – Inji Yariman Bakura

1423
0
Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura, Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara
Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura, Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara

Tsohon gwamnan jihar Zamfara Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura ya ce rikicin siyasar jihar ya jefa shi cikin tsaka mai wuya.

A hirarsa da kafar BBC, tsohon gwamnan, ya ce ya san an yi kuka da shi saboda wasu na ganin ya goyi bayan wani bangare, sai dai abin bah aka yake ba, shi ya tsaya ne a matsayin Uba

Karanta Labaru Masu Alaka: Na Daina Zuwa Jaje A Zamfara – Yariman Bakura

Tsohon mataimakin gwamna Yari, Ibrahim Wakalla, wanda na hannun damar Yarima ne, yana cikin ‘yan takara takwas da ake kira G8 da suka raba gari da tsohon Gwamnan Yari, bayan ya raba kujerun takara ga wadanda yake so a matakin gwamna da na ‘yan majalisa da suka kunshi har da ‘ya’yan Yarima.

Ya ce shi ya ba tsohon Gwamnan jihar Abdul’aziz Yari Abubakar kujerar shi ta Sanata, sannan ya amince masa ya fitar da dan takarar gwamna, lamarin da shi ne musabbabin rikicin.

Karanta Labaru Masu Alaka: Yariman Bakura Ya Sha Alwashin Ba Matawalle Goyon Baya

Wanda wannan ne yasa wasu suka zargi Sanata Yarima, da yin fuska biyu, inda aka rasa alkiblar sa.

Leave a Reply