Gwamnatin tarayya, ta ce tana duba yiwuwar kama wasu jami’ai da take zargi da hannu a wani hukunci da kotun Birtaniya ta yanke, inda ta bukaci gwamnatin ta biya wani kamfani tsabar kudi dala biliyan 9, saboda ta saba yarjejeniyar da ta kulla da shi.
Wata kotu a Landan ce ta yanke hukuncin cewa gwamnatin Najeriya ta biya kamfanin Process & Industrial Developments Ltd wadannan kudade sakamakon kwace masa kadarori.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya ce lamarin tsohuwar shari’a ce da ta faro tun a gwamnatocin baya da suka gaza wajen daukaka kara a kai.
Garba Shehu, ya zargi jami’an gwamnatin baya da yin sakaci kan abin da ya kira hadin baki dan a cuci Najeriya.
Ya ce duk da cewa gwamnati za ta daukaka kara amma abu na farko da za a yi shi ne duk wani wanda aka san da hannun sa a hadin bakin, gwamnati za ta dauki mataki akan sa. �
You must log in to post a comment.