Home Labaru Italiya: Ana Zargin Ministan Cikin Gida Da Tauye Hakkin ‘Yan Ci Rani

Italiya: Ana Zargin Ministan Cikin Gida Da Tauye Hakkin ‘Yan Ci Rani

245
0

Masu gabatar da kara a Italiya, sun soma gudanar da bincike, kan ministan cikin gidan kasar Matteo Salvini, bisa zarginsa da amfani da karfin ikonsa ta hanyar da bata dace ba, bayan haramtawa jirgin ruwan agajin da ya ceto ‘yan ci rani daga teku shiga cikin kasar.

Karanta Wannan: Karbo Kudade: Gwamnatin Tarayya Na Kokarin Kalubalantar Hukuncin Kotun Burtaniya

Rahotanni sun ce ‘yan sanda sun sama bincike kan muryoyin da aka nada ta wayar tarho, na musayar bayanai tsakanin ma’aikatar cikin gidan kasar ta Italiya, da kuma jami’an tsaron gabar teku.

A ranar asabar, ministan cikin gidan na Italiya ya baiwa kananan yaran da basa tare da iyayensu guda 27, daga cikin ‘yan ci rani sama da 100 da aka ceto daga tekun Mediterranean damar shiga cikin kasar, inda yacesaura 107 za su ci gaba da zama a gabar tekun.

Cikin wasikar da ya aikewa ofishin Fira Ministan kasar ta Italiya, Salvini ya ce ya bada umarnin ne ba a son ransa ba, sai dai ya sha alwashin ragowar ‘yan ci ranin manya 105 da kuma yara biyu, za su ci gaba da zama a gabar tekun kasar, cikin jirgin ruwan agajin da ya ceto su, matakin da ya gamu da sukar kungiyoyin agaji.