Home Labaru Kiwon Lafiya Fashi: ‘Yan Daba Sun Tada Hatsaniya A Wasu Sassan Jihar Saboda An...

Fashi: ‘Yan Daba Sun Tada Hatsaniya A Wasu Sassan Jihar Saboda An Kara Dokar Kulle

2564
0

Hayaniya ta barke a wasu sassam jihar Legas sakamakon matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na tsaiwaita dokar zaman gida a jihohin Legas da Ogun da kuma Abuja.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta tsawaita dokar ne  domin hana yaduwar cutar COVID-19 a Nijeriya, matakin da bai yi wa wasu mutanan yakin Legas dadi ba.

Wata majiya ta ce, ta’adin da aka yi a ranar Litinin ya yi kama da abin da ya auku a ranar Lahadi, inda wasu ‘yan fashi da makami a jihohin Legas da Ogun su ka rika fasawa mutane shaguna da gidaje.

Idan dai ba a manta ba, a ranar 12 ga Watan Afrilu wasu ‘yan fashi dauke da makamai sun yi wa mutanan yankunan Mangoro da Ogba da Agege da Iyana Ipaja da kuma Dopemu sata da daddare.

Fustattun matasan sun shiga duk wani lungu da sako unguwannin Legas inda suka rika huce fushin su a kan mutanan da ba su ji ba su gani ba.

Wani mazaunin kauyen Aluminium da ke garin Dopemu ya shaidawa manema labarai cewa, ‘yan fashin sun iso yankin su a kan babura 30 da motoci fiye da 100 da misalin karfe 7 ya yamma, inda su ka rika fasa shaguna da gidajen mutane.