Home Labaru Kurungus: Femi Fani-Kayode Ya Sauya Sheka Zuwa Jam’Iyyar Apc

Kurungus: Femi Fani-Kayode Ya Sauya Sheka Zuwa Jam’Iyyar Apc

10
0
Femi

Tsohon ministan surufin jiragen sama Femi Fani-Kayode ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.

An dai gabatar da Fani-Kayode a gaban shugaba Muhammadu Buhari a fadar sa da ke Abuja, bisa jagorancin shugaban riko na jam’iyyar APC kuma gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni.

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle na daga cikin wadanda su ka karbi Fani-Kayode a jam’iyyar APC.

Femi Fani-Kayode, ya ce akwai dalilan da su ka tilasta ma shi sauya sheka daga PDP zuwa APC, kuma daga ciki akwai neman hadin kan kasa.