Home Labaru Kuntatawa: Ruwan Leda Ya Yi Tashin Gwauron Zabo A Abuja

Kuntatawa: Ruwan Leda Ya Yi Tashin Gwauron Zabo A Abuja

6
0
Mazauna birnin Abuja sun fara kokawa bayan farashin ruwan leda ya yi tashin gwauron zabo inda aka koma sayar da leda guda a kan Naira 20 zuwa Naira 30.

Mazauna birnin Abuja sun fara kokawa bayan farashin ruwan leda ya yi tashin gwauron zabo inda aka koma sayar da leda guda a kan Naira 20 zuwa Naira 30. 

Masu sana’ar sun bayyana cewa yanzu ana sayar wa ’yan sari jaka guda na ruwan leda a kan Naira 200; ’yan tireda kuma suna sayar da leda a kan N20 zuwa N30, jaka kuma N250 zuwa 300.

Wata mai sayar da abinci a unguwar Utako a birnin Abuja, Ime Samson, ta shaida mana cewa, “Yanzu N20 take sayar da ledar ruwa; a da N100 zuwa N120 muke sayen jaka, amma yanzu ya koma N300 zuwa N350. To nawa ake so mu sayar

Ime ta ta kara da cewa yanzu ledan ruwa ya koma N20, a wasu wurare kuma ya kai N30.

Tsadar ruwan ta biyo bayan yajin aiki da kungiyar masu sarrafa ruwan leda a yankin Abuja suka gudanar, wanda tun kafin shi ake ta hasashen za su kara farashi.

Tun a lokacin sun yi ta korafin da suke yi game da tashin kayan hadi da rashin kyakkyawan yanayin kasuwanci da suka ce ba zai bari su ci gaba da gudanar da sana’ar tasu yadda aka saba ba.

Tun kafin yajin aikin da masu gidajen ruwa suka yi ake kokawa game da tsadar kaya hadi da sauran mastaloli da suka ce ba zai bari su ci gaba da gudanar da sana’ar tasu yadda aka saba ba.