Home Labaru Gargadi: Gwamnatin Jihar Legas Ta Koka Kan Yadda Gidajen Rawa Na Damun...

Gargadi: Gwamnatin Jihar Legas Ta Koka Kan Yadda Gidajen Rawa Na Damun Dattijai

6
0

Gwamnatin Jihar Legas ta gargaɗi gidajen casu da wuraren shan barasa su rage damun mutane da hayaniya ko kuma su fuskanci hukunci.

Hukumomi sun ce dattawa mazauna unguwar Lekki da ke maƙotaka sun sha kai musu kuka game da ƙara, wadda suka ce tana shafar lafiyarsu.

Wata sanarwa ta ce hayaniyar na faruwa ne “a kowane dare har zuwa asuba”.

Sanarwar ta ƙara da cewa an kama mutane a wasu wurare a Lekki, inda jami’an tsaro suka rufe wurin casu na Prest Jazz Club da aka samu suna amfani da “manyan lasifiƙoƙi”.

A watan Nuwamban shekar 2019 ma gwamnatin jihar ta rufe wasu masallatai da coci-coci saboda suna amfani da lasifika masu ƙara.