Home Labaru Sadarwa: Yadda Whatsapp, Instgram Da Facebook Suka Shafe Awa 6 Basa Aiki

Sadarwa: Yadda Whatsapp, Instgram Da Facebook Suka Shafe Awa 6 Basa Aiki

162
0
Kafofin sada zumunta na WhatsApp, Instagram da Facebook sun shafe tsawon awanni shida basa aiki, wanda hakan ya jefa mutanen dake amfani da su cikin damuwa.

Kafofin sada zumunta na WhatsApp, Instagram da Facebook sun shafe tsawon awanni shida basa aiki, wanda hakan ya jefa mutanen dake amfani da su cikin damuwa.

Shafuka da manhajojin WhatsApp, Instagram da Facebook wadanda dukkanninsu mallakin kamfanin Facebook ne, wanda kuma shi ke gudanar da su, sun daina aiki ne da misalin karfe 5:00 na yammacin ranar Litinin.

Lamarin ba iya Amurka, Birtaniya da nahiyar Turai kadai ya shafa ba, har sauran sassa na duniya.

Masu amfani da manhajoji ko shafukan WhatsApp, Instagram da Facebook, sun kasa turawa ko karbar sakonni ta nan, amma sauran kafafen sada zumunta irin su Twitter, TikTok, da Telegram suna aiki babu wata matsala.

Wannan shi ne karo na biyu da kafafen suka daina aiki a cikin kasa shekara guda, ko a ranar 19 ga watan Maris 2021, kafafon sun samu irin wannan matsala inda suka daina aiki har na tsawon sa’a biyu.

Leave a Reply