Hadaddiyar kungiyar kwadago ta Nijeriya wato NLC da TUC, ta bukaci gwamnatin tarayya ta kara wa’adin ritaya daga aiki zuwa shekaru 65 na rayuwa da kuma 40 na aiki.
Wannan dai, ya na daga cikin manyan bukatun da kungiyar ta gabatar a bikin ranar ma’aikata ta bana.
A tsarin aiki a Nijeriya dai, ma’aikaci zai yi ritaya idan ya kai shekaru 60 na rayuwa, ko kuma daga fara aiki ya kai shekaru 35,wanda hakan ke sa ake ganin ma’aikaci da sauran kuzarin sa amma dole ya ajiye aiki.
Shugaban kungiyar ma’aikatan kamfanoni ta TUC Komred Festus Osifo, ya bukaci gwamnatin tarayya ta kara shekaru 5 ga kowane bangaren mai ritaya kamar yanda ta yi ma wasu sassan aikin gwamnati.
Osifo, ya nuna takaicin yadda ake samun matsalar rashin samun kudin ajiye aiki, wadanda ma’aikaci kan yi amfani da su wajen sayean gida ko samun jari bayan ya yi ritaya. Nijeriya dai ta na daga cikin kasashen da mafi karancin albashi ba zai iya sayen rabin buhun shinkafa a wasu jihohin ba, inda a wasu kuma sai an samu ciko kafin a samu buhun