Wasu mahara da ake zargi ‘yan bindiga ne, sun hallaka mutane biyu tare da sace wasu hudu a yankin Kofar Kona da ke garin Zariya.
Rahotanni sun ce, maharan da su ka shiga unguwar da misalin karfe 9.40 na dare sun kai kimanin mutane 50.
Wani mazaunin unguwar da ya bukaci a sakaya sunan shi ya ce mayakan sun kai su hamsin, kuma da isar su su ka zarce gidan wani jami’in Kwastam mai suna Mallam Abubakar Modibbo.
Ya ce sun yi awon gaba da matar sa Asiya Abubakar da ‘ya’yan shi mata guda biyu, daga nan su ka yi awon gaba da wani magidanci mai suna Mallam Falalu Ibrahim.
Wani dan kungiyar sa-kai da ya bukaci a boye sunan sa, ya ce bayan maharan sun kammala da unguwar, sun kuma zarce zuwa kauyen Dorayi, inda su ka yi awon gaba da shanu masu yawa da mutane sama da ashirin.
Sai dai ya ce sakamakon musayar wutar da su ka yi da ‘yan sintiri, ‘yan bindigar sun tsere sun kyale wadanda su ka yi garkuwa da su.