Kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC, ta umarci ‘ya’yan ta da
kungiyoyin da ke karkashin ta da sauran ma’aikatan gwamnati su shirya yin zanga-zangar da za a yi a fadin Nijeriya daga ranar 27 ga watan Janairu zuwa 1 ga watan Fabrairu bisa shirin gwamnatin tarayya na cire tallafin man fetur.
Haka kuma, kungiyar ta bukaci duk kungiyoyin da ke karkashin
ta a fadin Nijeriya su umarci ‘ya’yan su domin tabbatar da
zanga-zangar da za a yi ta kasa baki daya.
Wannan dai shi ne babban dalilin yin wani taro da shugaban
kungiyar NLC Ayuba Wabba ya yi da shugabannin kungiyoyin
da ke karkashin Kungiyar kwadago a Abuja.
Wani dan kwamitin ayyuka da ya bukaci a sakaya sunan sa, ya
ce duk wani shugaba ko sakataren kungiyoyin da ke karkashin
kungiyar NLC ya lashi takobin cewa za su gudanar da zanga-
zangar.