Home Labaru Kuma Dai: Gwammanonin Kudancin Nijeriya Sun Bukaci Ikon Karbar Harajin VAT

Kuma Dai: Gwammanonin Kudancin Nijeriya Sun Bukaci Ikon Karbar Harajin VAT

12
0
Southern Gov

Kungiyar Gwamnonin Kudancin Nijeriya, sun bayyana goyon bayan su ga shirin maida ikon karbar harajin VAT a hannun gwamnatocin jihohi.

Gwamnonin sun bayyana goyon bayan su ne, yayin wani taro da su ka gudanar a garin Enugu.

Harajin VAT dai na taimakawa matuka wajen sama wa gwamnatoci kudaden haraji daga jama’a, wadanda ke fitowa daga cinikayyar da mutane ke yi.

Akasarin jihohin Nijeriya dai sun dogara ne da kudaden da su ke samu daga gwamnatin tarayya wajen gudanar da manyan ayyuka da kuma biyan albashin ma’aikata, sabanin jihohi irin su Lagos da Rivers da ke bada gudunmuwar akalla kashi 70 cikin 100 na kudaden harajin VAT da ake tarawa a asusun tarayya.