Home Labaru An Gudanar Zanga-Zanga Game Da Rashin Tsaro A Jihar Bauchi

An Gudanar Zanga-Zanga Game Da Rashin Tsaro A Jihar Bauchi

11
0

Wasu mazauna unguwar Birshin Fulani da ke cikin garin Bauchi, sun tare hanyar Bauchi zuwa Dass su na zanga-zanga dangane da tabarbarewar tsaro a yankin.

Wata majiya ta ce, lamarin ya janyo cunkoson ababen hawa, inda hanya ta toshe sakamakon tare hanya da masu zanga-zangar su ka yi.

Kusan makonni biyu da su ka gabata dai wasu ‘yan bindiga sun kai hari a yankin, inda su ka kashe mutane biyu, ciki har da wani babban ma’aikacin Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Bauchi Malam Abubakar Muhammad.

Haka kuma, an yi garkuwa da wasu mutane da dama a harin, sannan kwanaki kadan bayan faruwar lamarin aka kara sace wasu karin mutane.